Kipyegon ta ci zinare a gudun mita 1,500

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kipyegon ita ce wadda ta lashe gudun gasar Commonwealth

Faith Kipyegon ta lashe lambar zinare a gudun mita 1,500 a gasar Olympic da ake yi a birnin Rio na Brazil.

Kipyegon 'yar Kenya, ta kammala gudun a minti hudu da dakika 8.92, yayin da Genzeba Dibaba ta Habasha ta yi ta biyu.

Jenifer Simpson ta Amurka ce ta karbi tagulla a matsayin wadda ta yi ta uku a cikin minti hudu da dakika 10.

Labarai masu alaka