Brazil ta kai wasan karshe a tamaular maza

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption karo na hudu kenan Brazil tana kai wa wasan karshe a kwallon kafa a wasannin Olympic

Neymar ya ci kwallon da aka zura a cikin sauri a tarihin gasar kwallon kafa a wasannin Olympic, bayan da Brazil ta doke Honduras 6-0.

Neymar din ya ci wa Brazil kwallon farko a dakika 14 da fara karawa a wasan daf da karshe da suka yi a ranar Laraba.

A karawar kwallaye biyu Neymar da Gabriel Jesus suka ci sai Marquinhos Luan da kowannensu ya ci kwallo guda-guda.

Hakan ne ya ba wa kasar damar kaiwa wasan karshe a gasar Olympic, kuma karo na hudu kenan bayan 1984 da 1988 da kuma 2012.

A ranar Juma'a ne Brazil za ta buga wasan karshe da Jamus wadda ta doke Nigeria da ci 2-0 a wasan daf da karshe.

Labarai masu alaka