Kipruto ya lashe gudun mita 3,000

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun daga shekarar 1984 Kenya ke lashe gudun mita 3,000 a wasannin Olympic

Dan kasar Kenya, Conseslus Kipruto, ya ci lambar zinare a gudun mita 3,000 a wasannin Olympic da birnin Rio ke karbar bakuncin.

Dan wasan ya lashe gudun a minti takwas da dakika 3.28, yayin da dan Amurka Evan Jager ya ci lambar azurfa.

Mai rike da kambun Ezekiel Kemboi ne ya yi na uku, sai dai kuma an soke fafatawar da ya yi, bisa fita daga shatin layi a lokacin gudun.

Hakan na nufin dan kasar Faransa, Mahiedine Mekhissi-Benabbad ne ya ci lambar tagulla.

Kenya ta ci gaba da cin gudun mita 3,000 tun lokacin da ta lashe zinare a gasar Olympic da aka yi a Los Angeles a shekarar 1984.

Labarai masu alaka