Liverpool ta amince ta sayar da Benteke

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Benteke ya koma Liverpool a shekarar 2015 daga Aston Villa

Liverpool ta amince ta sayar da Christian Benteke ga Crystal Palace kan kudi fan miliyan 27.

Dan kwallon mai shekara 25, ya isa Landan domin a duba lafiyarsa kafin ya saka hannu kan yarjejeniya a Palace.

Benteke ya koma Liverpool da taka leda a shekarar 2015 kan kudi sama fan miliyan 32 daga Aston Villa.

A ranar Talata Liverpool ta ki sallama tayin da Palace ta yi wa Benteke kan kudi fan miliyan 23.

Labarai masu alaka