Semenya ta kai wasan karshe a tseren mita 800

Image caption A ranar Lahadi za a yi wasan karshe a tseren mita 800 na mata

'Yar kasar Afirka ta Kudu, Caster Semenya, ta kai wasan karshe a tseren mita 800 a wasannin Olympic da ake yi a birnin Rio na Brazil.

Mai shekara 25, wadda ta ci azurfa a gasar da aka yi a Landan a shekarar 2012, ta kammala tseren a matsayi na daya a minti daya da dakika 58.

Ita ma 'yar Birtaniya, Lynsey Sharp ta kai wasan karshe, sai dai kuma Shelayna Oskan-Clarke ta Birtaniya ta kai wasan karshen ba.

A ranar Lahadi ake sa ran fafatawa a tseren mita 800 na mata, domin fitar da wadan da za su lashe lambobin yabo a wasa.

Labarai masu alaka