Real Madrid ta fara La Ligar bana da kafar dama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid za ta karbi bakuncin Celta Vigo a wasa na biyu

Real Madrid ta fara buga gasar La Ligar Spaniya bana da kafar dama, bayan da ta doke Real Sociedad har gida a ranar Lahadai.

Madrid din ta ci kwallaye 3-0 kuma Gareth Bale ne ya ci biyu, yayin da Marco Asensio ya zura daya a raga a karawar.

Magoya bayan Sociedad sun yi ta tafi tsawon minti tara, domin jimamin mutuwar tsohon dan wasansu Dalian Atkinson, wanda ya mutu a ranar Litinin.

Atkinson wanda ya buga wa Sociedad tamaula daga tsakanin 1990-91, ya saka riga mai lamba tara a lokacin.

Labarai masu alaka