'Yan kwallon Nigeria sun samu tukwicin dala 390,000

Image caption Tun daga Japan Katsuya Takasu ya je Rio ya kuma ba su kudin da ya yi musu alkawari

An bai wa matasan Nigeria 'yan kasa da shekara 23 na Nigeria da tukwicin dala 390,000, bayan da suka ci tagulla a kwallon kafa na maza a Brazil.

Nigeria ta doke Honduras da ci 3-2 a wasan neman mataki na uku da suka fafata a ranar Asabar.

Wani kwararren likitan fida dan kasar Japan, Katsuya Takasu, ya cika alkawarin da ya yi wa 'yan wasan, bayan da ya tausaya musu kan halin da suka shiga na kin biyansu alawus-alawus dinsu.

Takasu ya mika wa Samson Siasia dala 200,000 da kuma dala 190,000 ga Mikel Obi a madadin 'yan tawagar Nigeria.

Ya kuma mika musu kudin ne awa biyu da Nigeria ta doke Honduras ta kuma lashe tagullar da kasar ta ci a gasar Olympic da aka yi a Brazil.

Daga cikin kudin da ya bayar dala 200,000 za su raba a matsayin alawus-alawus da ladan buga wasa, sauran dala 190,000 za su raba ne a domin lashe tagulla da suka yi.

Labarai masu alaka