Olympics: Ɗan Ethiopia na tsoron komawa gida

Hakkin mallakar hoto
Image caption Feyisa dai ya dora hannu daya kan daya alamun nuna adawa ga gwamnatin Ethiopia

Feyisa Lilesa, shi ne dan wasan gudun yada-kanin-wani da ya ciyo wa Ethiopia lambar yabo ta azurfa, a gasar wasannin Olympics da aka kammala a birnin Rio na Brazil.

Kuma bayan samun nasarar da ya yi , Lilesa ya daga hannuwansa ne sama ya kuma ratsa daya kan daya, wadda alama ce ta nuna goyon baya ga al'umar Oromo , wadda kabilar da ya fito ne a cikinta.

Sai dai kuma gwamnatin kasar tasa ba ta ji dadi ba kasancewar hakan wata alama ce ta nuna adawa ga gwamnatin.

Yanzu haka dai ya ce yana tsoron komawa gida, domin rayuwarsa na cikin hadari.

To amma gwamnatin ta Ethiopia ta ce za a yi masa tarba irin ta gwaraza, sannan babu abin da zai same shi.

Tuni dai kasashen duniya suka yaba matakin da ya Feyisa ya dauka , inda wasu ke cewa shi ne dan wasan Olympic da ya fi nuna jaruntaka.

Labarai masu alaka