Ina tausaya wa Joe Hart — Allardyce

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Joe Hart dan kasar Ingila ne

Kocin kungiyar wasa ta Ingila, Sam Allardyce ya damu da halin da golan Manchester City, Joe Hart yake ciki.

Har yanzu, Hart, mai shekara 29 dai bai tsare wa kulob din raga ba ko da sau daya a wasanni biyun da Man City ta taka a kakar wasannin bana ta Premier.

Bugu da kari, kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya ba wa Joe zabin ko ya bar kulob din ko kuma ya zauna.

Allardyce ya ce " akwai damuwa sosai."

To amma Allardyce ya ce Joe Hart zai kasance a jerin 'yan wasan Ingila da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kwallon Kafa ta Duniya, a wata mai kamawa.

Labarai masu alaka