Everton na zawarcin Lucas Martinez

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lucas Perez Martinez ya ce zai zauna har shekara guda a Everton

Kulob din Everton na zawarcin dan wasan Deportivo La Coruna, Lucas Perez Martinez domin ya zama mai taimaka wa Romelu Lukaku, a kan £15m.

Darektan kulob din, Steve Walsh ya dade yana sha'awar daukar Lucas, mai shekara 27 wanda ya zura kwallaye 17 a gasar La Ligar da ta gabata.

Sai dai kuma ana rade-radin cewa Romelu Lukaku yana son komawa tsohon kulob dinsa na Chelsea.

To amma Koeman ya tabbatar da cewa Lukaku ya fada masa ranar Juma'a cewa yana son cigaba da zama a Everton, akalla shekara guda.

Labarai masu alaka