Everton ba ta zawarcin Joe Hart — Koeman

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Joe Hart a lokacin wasan Man City da Bucharest ranar Laraba.

Kocin Everton, Ronald Koeman ya ce ba shi da niyyar sayen golan Manchester City, Joe Hart.

An dai ta alakanta Joe mai shekara 29 da zuwa Everton a kan aro, tun bayan da kocin Man City, Pep Guardiola ya fada ba shi zabin cigaba da zama a kulob din ko ya bari.

A ranar Laraba ne dai Joe Hart ya fara tsare ragar Man City a wannan kakar kuma ana tunanin karshen wasansa ke nan a kulob din.

Man City din dai na gab da kammala sayen golan Barcelona, Claudio Bravo mai shekara 33.

Koeman ya ce " kowa zai ga 'yan wasan Everton bayan kammala saye da sayarwar 'yan wasa a wannan makon."

Labarai masu alaka