Kafa Super League zai janyo yaƙi — Caferin

Image caption Manyan kungiyoyin wasa ne ke san kafa Super League

Dan takarar neman shugabancin Hukumar Kwallon Kafar Turai ta Uefa, Alexander Caferin ya ce yunkurin kafa wata sabuwar gasar kwallon kafa ta manyan kungiyoyin wasan kwallon kasashen Turai mai suna Super League, ka iya haddasa gaba tsakanin kungiyoyin.

Wannan dai na cikin alkawurra fiye da 20 da ya yi wa mutanen da yake neman kuri'arsu.

An kwashe watanni ana tattaunawa tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya tare da Uefa kan batun kafa European Super League.

Ana sa ran a ranar Juma'a ne za a fitar da matsaya kan tattaunawar wanda kuma ake kyautata zaton ka iya kawo karshen kokarin da wasu kungiyoyi suke yi na kafa Super League kafin 2021.

Alexander Caferin dai ya jagoranci hukumar Kwallon Kafa ta kasar Slovenia.

Labarai masu alaka