Thierry ne sabon mataimakin manajan Belgium

Hakkin mallakar hoto EPA

An nada tsohon dan wasan Arsenal da Barcelona da kuma Faransa, Thierry Henrya a matsayin mataimakin manajan kulub din Belgium.

Ya shiga kungiyar da ke horo ta Roberto Martinez, wanda ya maye gurbin Marc Wilmots a farkon watan Agusta.

Tsohon shugaban kulub din Everton, Martinez ya ce "Thierry mutun ne mai muhimmanci. " Zai kawo mana sabon abu. Ya yarda ya yi aiki tare da mu ba tare da wani shakku ba.

Henry mai shekara 39, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewar " Naji dadin matsayin mataimakin koci, na yi murna kwarai, na zaku."

Henry zai yi aiki tare da Graeme Jones wanda suka yi aiki tare da Martinez a Swansea da Wigan da kuma Everton.

Labarai masu alaka