Bahagon Fandam da Nuran Dogon Sani sun dambata

Image caption Turmi uku da suka taka babu kisa a tsakaninsu

Shagon Bahagon Fandam da Nura Shagon Dogon Sani sun dambata a ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Karawar tsakanin Shagon Bahagon Fandam daha Kudu da Nura Shagon Dogon Sani daga Arewa sai da suka yi turmi uku, amma babu kisa Sarkin Giga ya raba su.

Tun da farko Garkuwan Sojan Kyallu daga Arewa ne ya buge Garkuwan Bahago Mai Maciji daga Kudu, Abba Shagon Samsu daga Arewa ma doke Dogon Minista daga Kudu ya yi a turmin farko.

Bahagon Abban Na Bacirawa ma daga Arewa bugee Bahago na Balbali daga Kudu ya yi shi ma a turmin farko.

Sauran wasannin da aka yi canjaras sun hada da karawa tsakanin Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Shagon Autan Faya daga Kudu

Kadiri daga Arewa da Dan Matawallen Kwarkwada daga Kudu, da kuma sa zare da aka yi tsakanin Shagon Inda daga Arewa da Shagon Autan Sikido daga Kudu.

Labarai masu alaka