Leicester City na son daukar Slimani

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Leicester City ta ci wasa daya daga cikin uku da ta yi a Premier

Leicester City mai rike da kofin Premier da aka kammala na tattaunawa da Sporting Lisbon kan batun daukar Islam Slimani.

Sporting na bukatar a biya ta fan miliyan 34.1 kan dan wasan tawagar Algerian, mai shekara 28, yayin da Leicester ta ce farashin yi yawa matuka.

Slimani ya koma Sporting da murza-leda tun a shekarar 2013, ya kuma ci mata kwallaye 31 daga wasanni 46 da ya buga mata.

Dan kwallon ya buga wa tawagar Algeria wasanni hudu a gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil a shekarar 2014, inda ya ci kwallaye biyu.

Labarai masu alaka