3SC ta doke Kano Pillars da ci 4-0

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption An buga wasannin mako na 33 a gasar Firimiyar Nigeria

Shooting Stars ta ci Kano Pillars 4-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 33 da suka fafata a ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga a ranar Lahadin, Rivers United ta ci Plateau United 2-0, sai Ikorodu United da El-Kanemi Warriorsa da suka tashi kunnen doki.

Ifeanyi Ubah kuwa daya mai ban haushi ta ci Wikki Tourists ta garin Bauchi.

Tun a ranar Asabar Enyimba ta doke Akwa United da ci 2-1.

Ga sakamakon wasannin ranar Lahadi:
  • Ikorodu Utd 1-1 El-Kanemi
  • Rivers Utd 2-0 Plateau Utd
  • Nasarawa Utd 1-0 Rangers
  • Ifeanyiubah 1-0 Wikki
  • Tornadoes 2-0 Lobi

Labarai masu alaka