Arsenal ta dauki Mustafi daga Valencia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan ya lashe kofin duniya a shekarar 2014 tare da Jamus

Arsenal ta sanar da daukar mai tsaron baya, Shkodran Mustafi daga kungiyar Valencia kan kudi fan miliyan 35.

Dan wasan tawagar Jamus ya fara taka leda a Hamburger SV a matsayin matashin dan kwallo daga nan ne ya koma Everton aro da wasa.

Daga nan ne ya koma Sampdoriya a watan Janairun 2012, kuma a watan Agustan shekarar 2014 ya koma Valencia.

Mustafi ya fara buga wa tawagar Jamus tamaula a karawar da ta yi da Poland ranar 13 ga watan Mayun 2014, yana kuma cikin 'yan wasan da suka ci wa kasar kofin duniya da aka yi a Brazil a 2014.

Labarai masu alaka