Bayanai kan cinikayyar 'yan kwallo da aka yi a bana

Hakkin mallakar hoto Getty

Kungiyoyin Premier sun kashe kudi sama da fam biliyan daya wajen sayen 'yan wasan kwallon kafa domin karfafa wasanninsu a gasar wasanni ta bana, in ji kamfanin Deloitte mai samar da bayanai a kan harkar wasanni.

A bara fam miliyan 870 suka kashe kwana biyar kafin kasuwar ta watse.

Kungiyoyin Premier suna fitar da makudan kudi domin sayo 'yan wasan tamaula, yayin da suke cin moriyar kudin da ake nuna wasannin gasar a talabijin da ya kai sama da fam biliyan biyar.

Hakan kuma ya sa kungiyoyi 12 sun kafa tarihin sayen 'yan kwallon da suka fi tsada a bana.

Dan wasan da aka saya mafi tsada a bana a duniya shi ne Paul Pogba daga Juventus zuwa Manchester United a kan kudi sama da fam miliyan 105.

Gonzalo Higuaín ne na biyu a tsada a bana daga Napoli zuwa Juventus a kan kudi sama da fam miliyan 90.

Dan kasar Brazil Hulk ne a mataki na uku wanda Zenit St. Petersburg ta sayarwa Shanghai SIPG ta China shi a kan kudi sama da dala miliyan 47.

Dan Afirka mafi tsada a bana shi ne Sadio Mané wanda Southampton ta sayarwa Liverpool shi a kan kudi sama da fam miliyan 41.

Hakkin mallakar hoto rex features

Eric Baily, dan wasan tawagar Code d'Ivoire, shi ne na biyu a tsada daga Afirka wanda ya bar Villarreal zuwa Manchester United a kan kudi sama da fam miliyan 38.

Dan Afirka na uku da aka saya da tsada a bana shi ne André Ayew na Ghana wanda ya koma West Ham United daga Swansea a kan kudi sama da fam miliyan 24.

Dan wasan da aka saya mafi tsada a Spaniya shi ne Andre Gomes daga Valencia zuwa Barcelona kan fam miliyan 50.

Hakkin mallakar hoto Getty

Gonzalo Higuain shi ne dan kwallon mafi tsada a Italiya wanda Napoli ta sayarwa da Juventus fan miliyan 90.

Hakkin mallakar hoto Getty

A jamus kuwa Mats Hummels shi ne wanda aka saya mafi tsada daga Borrusia Dortmund zuwa Bayern Munich kan fam miliyan 38.

Hakkin mallakar hoto Getty

Labarai masu alaka