Argentina za ta ziyarci Venezuela ranar Talata

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Argerntina ce ke mataki na daya, bayan da aka yi wasanni bakwai

Venezuela za ta karbi bakuncin Argentina a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a 2018.

Sai dai kuma Lionel Messi ba zai buga karawar ba sakamakon raunin da ya yi a fafatawar da Argentina ta ci Uruguay daya mai ban haushi a ranar Alhamis.

Bayan da rukunin Kudancin Amurkan ya yi wasanni bakwai daga 18 da zai yi, Argentina ce ta daya sai Uruguay sai Colombia sannan Ecuador, Brazil tana mataki na biyar.

Kasashe hudu ne za su samu gurbin buga gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 daga Kudancin Amurka kai tsaye, yayin da kasa ta biyar ta buga wasan cike gurbi.

Labarai masu alaka