World Cup 2018: 'Canada ta so yin cuwa-cuwa'

Image caption 'Yan wasan kasar Canada a lokacin wasansu da El Salvador

Kungiyar wasa ta El Salvador ta ce taki amincewa ta karbi cin-hanci domin ta yarda kungiyar wasa ta Canada ta ci ta, a wasan da za su yi ranar Talata.

El Salvador dai za ta kara da Canada ne a wasan zagayen karshe na ajin A, na neman gurbin shiga gasar kwallon kafa ta duniya ta 2018.

Dole ne dai Canada ta buge El Salvador a wasan da za su yi a Vancouver kafin ta samu gurbin shiga gasar.

Sannan kuma Mexico sai ta doke Honduras a wasan karshe na 'yan rukunin A.

Hakan ne kuma ya sa Canada neman ba wa El Salvador na goro domin ta ba ta dama.

A wani taron manema labarai, 'yan wasan na El Salvador sun nuna wani hoton bidiyo da suka dauka na wani mutum da suka zarga da neman ya ba su na goro.

Yanzu haka hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa ta ce tana bincike kan al'amarin.

Labarai masu alaka