Ya kamata Rooney ya yi ritaya — Shilton

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wayne Rooney lokacin wasan England da Russia a gasar Euro 2016

Tsohon kyafin fin kungiyar wasa ta Ingila, Peter Shilton ya ce ya kamata Wayne Rooney ya yi murabus daga kwallon duniya, bayan kammala gasar Euro 2016.

Rooney, mai shekara 30 ya taka wa Ingila wasa na 116 a ranar Lahadi lokacin wasan neman gurbin shiga gasar kwallon duniya da Slovakia.

Shilton ya ce "ba na tunanin har yanzu maciyin kwallo ne. Muna ta faman kokarin mu ga cewa ya rike kambunsa amma ban dauke shi a matsayin dan wasan tsakiya ba. Kuma ba zai taba zama ba."

Da yake magana da BBC, Shilton, mai shekara 66 ya kara da cewa " Yana kokarin taka leda amma ba na tsammanin yana da wani tasiri."

Labarai masu alaka