Shugaba Muhammadu Buhari na son gyara halayen 'yan Nigeria

Asalin hoton, AFP
Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo sauyi ta fannoni daban-daban
A ranar Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani shirin da aka yi wa take da "change begins with me" wanda ke nufin sai na sauya dabi'una za a samu sauyin da ake bukata.
Shugaban ya kaddamar da wannan shiri ne da nufin samun sauyi a dabi'un mutane, wanda ake sa ran hakan zai samar da cigaba a Najeriya.
Da yake kaddamar da shirin a fadarsa, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ce yanzu babu abin da ke tafiya dai-dai a kasar.
Ministan yada labarai na kasar, Lai Mohammed ya ce shirin zai ilmantar da mutane a kan mahimmancin kyautata dabi'u.
Ya ce shirin zai taimaka wajen farfado da kima da rikon amana da kuma kwatanta kyawawan hallaya, a duk inda mutum ya tsinci kansa.
Mista Lai ya kara da cewa shirin zai daga daraja da kimar kasar a idanun duniya.
A shekaru 31 din da suka gabata, a lokacin da Buhari yake mulkin soja, shugaban ya kaddamar da wani shiri makamancin wannan domin yaki da rashin da'a a kasar.
An yi wa shirin lakabi da 'War Against Indiscipline' wato Yaki da Rashin Da'a.
Manyan matsalolin da Najeriya ke fama da su, su ne rashawa da cin-hanci da rashin girmama dokokin kasa.
Sharhi
Wasu dai na ganin kamar shirin shugaban na yaki da rashin da'a ba shi ne mafi a'ala ba, a inda wasu ke cewa hakan ya dace.
'Yan kasar dai na fama da kuncin rayuwa sakamakon tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta samu kanta a ciki.
Masana dai na alakanta tabarbarewar tattalin arzikin da wasu tsare-tsaren gwamnati.
Gwamnatin Buhari dai ta cire kudaden tallafin man fetur da rage darajar Naira.