Mourinho zai karbi bakuncin Guardiola a gasar Premier

Gasa Premier Manchester

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Manchester City ce za ta ziyarci Manchester United

A ranar Asabar za a buga wasan mako na hudu a gasar Premier, inda Manchester United za ta karbi bakuncin Manchester City a Old Trafford.

Karawa ce ta hamayya tsakanin kungiyoyi biyu da ke birnin Manchester, masu buga wasannin Premier.

Kuma wasa ne na hamayya tsakanin kociyan Manchester United Jose Mourinho da mai horar da Manchester City, Pep Guardiola.

Mourinho da Guardiola sun hadu a wasanni sau 16 a tsawon shekara bakwai a kungiyoyi biyar da suka horar a tsakaninsu,

A haduwa 16 da suka yi Guardiola ya lashe wasanni bakwai, Mourinho kuwa guda uku ya ci sannan sun yi canjaras a fafatawa shida.

Masu horarwar sun hadu a lokacin da Guardiola ya horar da Barcelona da Bayern Munich, yayin da Mourinho ya koyar da Real Madrid da In ter Milan da Chelsea.