An dakatar da Lochte daga wasan linkaya

Wasanni Rio Linkaya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ryan Lochte ne ya bayar da sanarwar an yi musu fashi a Rio

An dakatar da dan wasan linkayar Amurka, Ryan Lochte, daga shiga duk wata gasa har tsawon watanni 10, bayan da ya yi karyar an yi masa fashi a birnin Rio a lokacin gasar Olympic.

Dan wasan mai shekara 32, ya ce da shi da wasu abokan linkayarsa uku aka yi wa fashin a wani gidan mai lokacin da suka fita shan iska da daddare.

Sai dai kuma wani faifan bidiyo da jami'an tsaro suka fitar ya nuna 'yan wasan suna lalata gidan man.

Hukumar linkaya ta Amurka da kwamitin Olympic na kasar sun dakatar da 'yan wasan uku da aka yi karya da su.