Gabon: Kotun tsarin mulki za ta sanar da sabon sakamakon zabe

Ministan cikin gida ne ya sanar da sakamakon zaben farko
Bayanan hoto,

Jean Ping ya shigar da kara a kotun tsarin mulki

Mutumin da sakamakon zaben kasar Gabon ya nuna ya sha kasa, Jean Ping ya shigar da kara a kotun tsarin mulkin kasar.

Shi dai mista Ping yana kalubalantar sakamakon zabe na wucin-gadi wanda ya bai wa abokin hamayyarsa, Ali Bongo nasara.

Ali Bongo wanda shi ne shugaban kasar mai-ci, ya yi nasarar lashe zaben na ranar 27 ga Agusta, bayan ya da kuri'un da ya samu suka zarta na Jean Ping da kimanin 6,000.

Alkalan babbar kotun kasar dai na da mako biyu domin yanke hukunci kan koken da dan takarar ya shigar, kafin sanar da wanda ya yi nasara a zaben mai cike da sarkakiya.

Ana tunanin cewa sanar da mutumin da ya lashe zaben da kotun za ta yi, ka iya haifar da sabon rikici ga bangaren da bai yi nasara ba.

Daman dai ministan ma'aikatar cikin gidan Gabon ne ya sanar da sakamakon zaben na wucin-gadi.

Hakan ne kuma ya kawo barkewar rikici a Libreville, babban birnin kasar da ma sauren wasu birane.