Me ke zaburar da ma’aikata a aikin da ba’a samun kudi?

Ma'aikata suna nazari
Bayanan hoto,

Ma'aikata suna nazari

In da za'a tambayi Robert Lee matsalar da ta ke damun ma'aikatarsa, zai ce ma'aikatansa sun fiye azama.

Lee ya na gudanar da wani kamfanin taimakon al'umma ne mai suna Rescuing Leftover Cuisine, wanda kan karbi abincin da ba'a cinye ba a shagunan sayar da abinci, ya rarraba ga kungiyoyin da ke ciyar da mabukata a jihohi 12 na kasar Amurka.

Idan ka ji wayarsa ta kada, mafi yawan lokuta, wani shagon abinci ne zai sanar da shi akwai ragowar abinci, kuma nan take ma'aikatansa zasu fara rige-rigen zuwa su karbo.

Bayanan hoto,

Kwashe ragowar abincin da aka bari a gidan cin abinci don ba almajirai

Tun daya bar aikinsa na mai nazarin kudi a kamfanin JP Morgan shekaru biyu da suka wuce domin tafiyar da wannan kamfanin taimakon, Lee ya gano cewa ma'aikatan kamfanonin da aka kafa ba don riba ba sun fi ma'aikatan kamfanonin kasuwanci hazakar aiki, amma abubuwan da ke zaburar da su sun bambanta da juna.

Su na yin aiki tukuru tare da taimakawa abokan hulda, amma ba don kudi ko daukaka ba. Maimakon haka, burinsu shi ne su taimakawa mutane masu yawan gaske.

Don haka maimakon rige-rigen fita da zarar an kira waya, Lee ya koya musu gudanar da aikin cikin tsari, yadda a fita daya za su dauko abinci daga wurare dabam-daban, abinda zai sa a yi amfani da mota da ma ma'aikatan yadda ya kamata.

Lee ya ce: "Ma'aikatana su na da matukar burin ba da gudunmawa, don haka duk abinda ya taso sai su ce zamu iya.

Amma wajibi ne a nuna musu muhimmancin amfani da lokaci domin samun cikakken tasiri."

Wannan darasi ne ga duk manajan da ke sauya wurin aiki daga kamfanin kasuwanci zuwa kamfanin tallafi, saboda mafi yawan ma'aikatan masu kishin jama'a ne, wadanda kudi ko samun daukaka ba sa gabansu.

Don haka idan zaka bar aikin kamfani ka koma wurin tallafawa jama'a, sai ka shirya ganin wata sabuwar hanyar tunanin yadda ake aiki da kuma yadda ake shugabantar ma'aikata.

Ba maganar kudi ba ce

Saboda ma'aikatan kamfanonin tallafawa al'umma na samun kaimi ne daga burinsu na cimma manufar da aka sa gaba, ya zama wajibi ga manajoji su samar da sababbin hanyoyin zaburar da su, in ji Taara Hoffman, daraktar gudanarwar GirlVentures, mai shirya wasanni da tafiye-tafiye ga 'yan matan da rayuwarsu ke cikin hatsari.

Maganar ba ta kudi ba ce.

Hoffmann, ta ce ma'aikatanta za su fi samun kudi idan su ka yi aiki a wasu wuraren dabam.

Haka kuma ba maganar mukami ba ce ko daukaka domin kuwa ma'aikata masu ilimi za su fi samun mukamai masu daraja a kamfanonin kasuwanci.

"Sirrin shi ne ka gano me ke zaburar da su kan aikinsu," in ji Hoffman.

Mafi yawan ma'aikatan kamfanonin tallafi ba su zo aiki domin samun damar cika bakin kammala wani shiri ko kuma samun karuwar kudin shiga kamar ma'aikatan sauran kamfanoni ba, in ji Lee.

"Saboda kowannensu ya damu da manufar, a shirye su ke su manta da girman kansu."

Maimakon haka, a cewar Hoffman, mafi yawan lokuta abinda ya ke zaburar da su shi ne dangantakarsu da manufar.

Da yawan ma'aikatanta na son taimakawa 'yan matan da ke rayuwa cikin talauci ne.

Wasu kuma an taba tallafa musu ne a baya su ke son su rama wa wasu.

Don haka Hoffman na kokarin gano abinda ke iza su sannan ta ba su aikin da ya dace da su.

Da zafi-zafi

Babu isasshen lokaci, in ji Leila Janah, shugabar kamfanin Sama Group, mai burin rage talauci a duniya ta hanyar taimakawa mutane su sami aiki a intanet.

Bayanan hoto,

Masu aiki a gidan sayar da abinci

Akwai ma'aikatan kamfanonin tallafi da yawa, wadanda fitarsu daga jami'a ke nan, su ka ware shekaru biyu zuwa uku su taimakawa jama'a kafin su yi gaba, zuwa inda za su sami kudi.

Wannan na nufin zaburar da ma'aikata cikin hanzari domin cin ma manufofinsu cikin dan kankanin lokaci.

Janah ta ce: "A matsayinka na manaja, samun sakamakon da ki ke so a kamfanonin tallafi yafi wuya.

Saboda sun ki yi bincike mai zurfi kafin gano abinda ke zaburar da kowanne ma'aikaci."

Wadansu na son taimakawa wadanda su ka fuskanci irin matsalolin da su ka fuskanta ne, wadansu kuma su na son taimakawa wani rukunin al'umma ne.

Idan ka gano wannan dalilin, to ka samo yadda za ka zaburar da ma'aikatanka, a cewar Janah.

Saboda haka, wajibi ne manajojin kamfanonin tallafi su ga cewa sun sama wa ma'aikatansu tsarin aiki mai kyau, in ji Janah.

Mafi yawansu su na dimbin kwarewa da tarin ilimi, don haka zai iya samun aiki a wasu wuraren nan take.

Bayanan hoto,

Mafi yawan ma'aikata a kamfanonin da aka kafa ba don samun kudi ba suna yi ba don neman su tara kudi ba

Wannan na nufin amincewa da wadansu abubuwan da ba za'a amince da su a kamfanonin kasuwanci ba, kamar sauyawa mutum tsarin aiki, yin aiki daga gida, yin aiki a lokutan da su ke so, da ba ku ba su damar yin wasu ayyukan na daban da su ke jin dadinsu a lokacin aiki ko da basu shafi aikin da aka sa su ba.

Misali wanda aka sa aikin amsa tarho, amma ya na son fita waje domin haduwa da mutane.

Bugu da kari, wajibi ne a rika tunawa ma'aikata kudirin da aka sa gaba, in ji Janah.

Idan za ki bai wa wani aikin da ba ya so, sai ki tuna masa yadda gudanar da wannan aikin zai taimaka wurin cimma kudirin da aka sa gaba.

Saboda a kamfanin da ba kudi ko daukaka ke zaburar da ma'aikata ba, wajibi ne manajoji su tuna da abu guda: kowa ya na yi ne domin cimma manufar kamfanin.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: What keep workers going when it is not all about money