Najeriya ta samu lambobin yabo 2 a Paralympics

A yanzu dai Najeriya ta samu lambobin yabo biyu kenan a gasar wasannin Paralympics ta nakasassu
Najeriya ta ci lambar yabo a wasannin ɗaga nauyi na maza da mata a gasar wasannin Paralympics ta nakasassu a birnin Rio de Janeiro.
Najeriyar ta samu zinare na farko ne daga wajen dan wasanta Ezuruike Roland a wasan ɗaga nauyi na maza.
Lambar yabo da Najeriyar ta fara ci a gasar dai shi ne azurfa a wasannin ɗaga nauyi na mata da Latifat Tijani ta lashe.
A yanzu dai kasar ta samu lambobin yabo biyu kenan a gasar wasannin Paralympics ta nakasassu.