Kasar Saudia ta fito da sabbin ka'idoji domin kaucewa afkuwar hadari

aikin hajji

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A na sa ran mahajjata ba za su fuskanci cunkoso a wajen jifa ba

Hukumomi a kasar Saudiyya, sun fito da wasu sabbin ka'idojin fita jifan shaiɗan.

Hukumomin sun fito da ka'idojin ne domin kaucewa afkuwar mummunar hadarin da ya faru a bara.

Sheikh Yusuf Yahaya Alibawa daya daga cikin malamai masu yi wa mahajjata jagora daga jihar Sakkwato a Najeriya, ya ce " bana mutane 250 ne kawai za a rika diba a lokaci guda daga shemarsu domin zuwa jifa."

Sai dai kuma mahajjata da dama ba su yi na'am da wannan sabon tsarin inda Sheikh Yusuf ya kara da cewa " mu ba haka muka so ba, mun so a ce alhazai su rika tafiya suna yi yadda suka saba, sai a dauki wasu matakai masu sauki."

A shekarar da ta gabata ne aka samu turereniya wadda ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.