Kotu bata soke sakamakon zabe ba a Nahiyar Afirka a cewar Robert Gerenge

Siyasar nahiyar Afirka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kotu bata saba soke sakamakon zabe ba a nahiyar Afirka

Kotu bata taba soke sakamakon zaben shugaban kasa ba a nahiyar Afrika, a cewar Robert Gerenge, shugaban shirye-shirye na musamman a cibiyar cigaban demokradiya na Afrika.

A shekarar da ta gabata, 'yan takara a kasar Uganda da Zambia da suka sha kaye a zabe sun gaza amfani da damar da suke da ita a kotu, duk da cewar hakan ba yana nufin ana magudi a dukkan zabukan ba ne.

A zaben shugaban kasar da aka yi a Zambia a watan Ogusta, matsalar na'ura ta hana yunkurin Hakainde Hichilema na canza sakamakon zabe saboda ya makara wajen gabatar da korafinsa.

A watan Maris ne kotun kolin kasar Uganda ta yi watsi da kalubalantar sakamakon da Amama Mbabazi ta yi duk da cewar akwai wasu matsaloli amma ba su shafi sakamakon ba.

Wannan hukuncin da kotun ta yanke ya taba faruwa a nahiyar a baya.

Bayan zaben da aka yi a Najeriya a shekarar 2007, tsarin shari'ar kasar yasa sai da aka shafe watanni 20 kafin kotu ta zartar da hukunci.

Kotun kolin ta ce duk da cewar an samu kura-kurai, amma babu wata shaidar da ta nuna cewar sun shafi sakamakon zaben.

A kasar Zimbabwe, da farko Morgan Tsvangirai ya garzaya kotu a shekarar 2013 domin ya kalubalanci sake zaben shugaba Robert Mugabe da aka yi.

Sai dai daga bisani ya janye karar da ya shigar, yana mai cewa shugaban kasar ya hana shi damar samun adalci a shari'ar.

Sai dai a cewar Mista Gerenge, akwai wasu yanayi uku dake faruwa:

Na farko magoya bayan 'yan adawa basu da kwarin gwiwa game da tsarin shari'a a don haka suke yin zanga-zanga maimakon su je kotu.

Na biyu shine 'yan takaran da suka sha kaye sukan garzaya kotu ne saboda matsin lamba ta fuskar diflomasiya duk da cewa ba su da kwarin gwiwa samun kyakyawar sakamako

Yayin da kuma wasu 'yan takaran da suka sha kaye na da kwarin gwiwar cewar alkalan za su yi musu adalci.