An soma aikin Hajji

Hajj, Saudi, Muslims

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mahajjata suna addu'oi a ka'abah

Kimanin musulmi miliyan ɗaya da rabi suna hallara a Saudi Arabia cikin tsauraran matakan tsaro domin soma gudanar da aikin Hajjin bana.

Motoci ba zasu iya zuwa kusa da masallacin ka'abah ba, kuma a wurare da dama 'yan sanda suna tatance maniyyata.

Abinda Saudiyya take fatan kaucewa shi ne sake faruwar abinda ya auku bara, inda mahajjata fiye da dubu biyu suka mutu sakamakon turmutsutusu.

Yawancin mahajjatan da suka mutu dai 'yan kasar Iran ne, kuma Iran ta zargi gidan sarautar Saudiyya da gazawa wajen tsara aikin Hajjin.

Tun a cikin daren jiya ne dai dubban mahajjatan suka fara turuwa zuwa sansanin Mina da ke wajen birnin na Makka kafin su wuce zuwa filin Arafa a gobe domin tsayuwar arfa wadda ita ce kololuwar aikin Hajjin.

Najeriya dai na daga cikin kasashen da ke adadin mahajjata mafi yawa da ke kasar ta Saudiyya domin aikin hajjin.