Yau ne al'ummar musulmi ke bikin babbar sallah

Ana yanka dabbobin layya bayan saukowa daga idi
Bayanan hoto,

Sallar layya na daya daga sallolin idi guda biyu da musulmi ke yi a shekara

A yau ne al'umar musulmi a fadin duniya ke gudanar da shagulgulan Babbar Sallah, daya daga cikin bukukuwa na shekara-shekara mafi muhimmanci a addinin Islama.

Ana bikin na Babbar Sallah ne yayin da dimbin Musulmin da suka samu sukunin zuwa aikin Hajji a kasar Saudiyya, ke kammala aikin na Hajjin.

Bayan kammala sallar idin dai musulmai masu hali za su yanka dabbobin layya.

A lokutan sallah dai jama'a na kai ziyarce-ziyarce ga 'yan uwa, gami kuma da rabon abinci da ake yi na musamman.

A bana dai bukuwan sallar na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Nijeriya ke fama da matsi na tattalin arziki, abin da ake gani zai iya rage armashin sallar a wajen wasu, musamman wadanda ba su damar yin layya ba.

Malaman addinin musulunci dai na kiraya-kiraye ga wadanda suka samu halin yin layyar da su taimaka wa wadanda ba su samu ikon yi ba da naman layya.