Amurka: Hillary Clinton ta kamu da cutar Pneumonia

Hillary Clinton ta fice daga wajen taron tunawa da harin 11 ga watan Satumba saboda rashin lafiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Hillary Clinton na fama da cutar Pneumonia

'Yar takarar shugabancin Amurka ta jam`iyyar Democrat, Hillary Clinton ta harbu da cutar Pneumonia.

Wata sanarwa ta ce a ranar Juma`ar da ta wuce ne cutar ta kama ta a wajen wani taro, inda Likitarta, Lisa Bardack ta tabbatar da hakan, bayan ta duba lafiyarta.

A cewar Likitar, Misis Clinton ta galabaita sosai a wajen bikin tunawa da harin 11 ga watan Satumba da aka yi a New York, kuma wannan ne ya sa ta yi saurin fita daga wajen taron.

Wani hoton bidiyon da aka sanya a intanet ya nuna yanda gwiwoyinta suka sankare, har aka tallafa mata wajen shiga mota, amma daga baya ta sake bayyana daga gidan diyarta, inda ta shaida wa manema labaru cewa ta samu sauki.

Sai dai wani mai rubuta wa tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan jawabi, Clark Judge ya ce da yiwuwar ta dauki lokaci kafin ta ci gaba da harkokinta:

Ya ce ka san Pneumonia ba karamar cuta ba ce, za ta iya hana ta yakin neman zabe na akalla mako guda, watakila har zuwa ranar zabe.

Tuni dai abokin hamayyarta, dan takarar jam`iyyar Republican, Donald Trump ya nuna damuwarsa game da lafiyar Misis Clinton din.