'Yan tawayen Syrai na nazarin yarjejeniyar tsagaita wuta

Amurka da Rasha ne suka rattaba a yarjejeniyar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan tawayen na nazarin yarjejeniyar

Kungiyoyin `yan tawaye a Syria sun yi gum da bakinsu dangane da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Rasha da Amurka, wadda ake sa ran za ta fara aiki yau din nan.

Har yanzu dai ba su fito fili sun ce za su martaba yarjejrniyar ba ko a`a.

Wasu rahotanni dai na cewa watakila kungiyar `yan tawaye mafi karfi mai suna Ahraral-Sham ta yi watsi da yarjejeniyar, saboda a ganin ta za ta yi wuyar aiwatarwa.

Kazalika wani jami`in wata kungiyar `yan tawayen ya ce sun yi na`am da yarjejeniyar dakatar da fada, da kuma yunkurin shigar da kayan agaji, amma suna da ja dangane da wasu batutuwan da yarjejejniyar ta kunsa.

A jiya Lahadi ma, an ba da labarin cewa jiragen yakin Syria da Rasha sun yi barin-wuta a lardin Aleppo da Idlib, kuma a ranar Asabar ma sama da mutum 100 aka kashe a wasu hare-haren.