'Za mu shafe birnin Pyongyang daga bayan kasa'

Kasashen duniya sun maida koriya ta arewa saniyar ware

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana zaman dar-dar a yankin Korea

Gwamnatin Koriya ta kudu ta yi gargadin cewa makwabciyarta, Koriya ta arewa na shirin sake jarraba wani makami mai linzami.

Wasu majiyoyin kwarraru sun yanke wannan hukuncin ne bayan sun yi nazarin wasu hotunan da aka dauka ta sama na wani yanki mai tsauni da Koriya ta arewar da ta saba yin gwajin makaman nata.

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Kudu Yonhap yace koriya ta arewa ta kammala dukkan shirye shiryen gudanar da wani gwajin ko wane lokaci daga yanzu.

Gwajin makamin mai linzami da koriyar ta arewa ta yi a ranar Juma'ar dai shine mafi girma cikin wadanda ta taba yi a baya, abinda kuma ya janyo suka daga kasashen yamma.

Wani mazaunin babban birnin koriya ta arewar Pyongyang Cho Yong Kuk yace a yanzu karan kasarsa ya kai tsaiko, kuma za ta iya kafada da duk wata kasa mai karfi a duniya.

To sai dai tuni koriya ta kudu ta yi barazanar shafe babban birnin koriya ta kudu Pyongyang daga bayan kasa, matukar ta yi gangancin nuna alamar kaddamar da harin makamin Nukiliya.

Wata majiyar sojan kasar ta shedawa kamfanin dillancin labaran Yonhap cewa za a durkusar da duk wani tsayayyen abu a birnin Pyongyang da makamai masu linzami, da kuma manya abubuwan fashewa.

Majiyar sojan ta ce za kuma a fi maida hankali gundumar da ake zaton cewa a nan ne shugabannin koriya ta arewan suke a duk lokacin da aka tashi kai harin.

Bayanan hoto,

Koriya ta Kudu ta yi barazanar shafe Korea ta Arewa daga bayan kasa

Koriya ta kudun ta kuma yi barazanar cewa za a mai da birnin Pyongyang toka, a kuma share shi daga taswirar duniya.

To sai dai masu lura da al'amura na ganin koriya ta kudun ta yi amfani ne da irin kalaman da koriyar ta arewa ta jima ta na yi a kanta na barazana da cika-baki.

Wasu bayanai dai na cewa tuni aka mikawa majalisar dokokin koriya ta kudu tsare-tsaren kai hari kan koriya ta arewa bayan gwajin da ta yi ranar Juma'a.

Kwamitin tsaro na MDD yace yana shrin kakabawa kooriya ta arewa karin tukunkumi, yayin da ita ma Amurka tace tana shirin daukar nata karin matakin daban.

To sai dai koriya ta arewar ta mai da martani kan barazanar takunkumin, inda tace ko a jikin ta, sannan tace barazanar abin dariya ce.