An yi sallar Idi lafiya a Jamhuriyar Niger

Shaikh Jibril Soumaila Karanta yana jagorantar sallar Idi a Masallacin Gaddafi dake birnin Yamai
Bayanan hoto,

Limamin Masallacin Gaddafi Shaikh Jibril Soumaila Karanta ya yi hudubar hadin kai

Al'ummar Musulmin Jamhuriyar Nijar sun bi sahun Musulmin duniya wajen gudanar da sallar Idi.

A babban masallacin Yamai, wanda aka fi sani da Masallacin Gaddafi, Liman Shaikh Jibril Soumaila Karanta, ya yi huduba da kira ga Musulmin Nijra su so kasarsu da junansu.

"Idan ka san akwai wani abu tsakaninka da dan uwan ka [to] ku nemi gafarar [juna]. Yau rana ce da ake so a yawaita sadaka, a ji tausayin miskinai, a kuma ba su goyon baya", inji Shaikh Karanta.

Shugaba Mahamadou Issoufou da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar na cikin wadanda suka yi sallah a masallacin.

Kakakin gwamnatin kasar, Asoumana Malam Issa, ya bayyana wa wakilin BBC Baro Arzika yadda ya ji kalaman babban limamin.

"Musulmi kowa ya san ranar layya rana ce wadda ya kamata wanda bai da karfi a kama mashi, kuma dangane da yanke-yanken da aka yi ma ya kamata a ce wadanda suka yanka su kai wa wadanda ba su yanka ba".

Sai dai kuma wadansu 'yan kasa kokawa suke yi da yanayin da sallar ta zo masu.

Wani talaka cewa ya yi: "Gaskiya akwai tsanani a wannan lokacin; a cikin ko wanne lamari akwai tsanani--ba kudi, ga mutane ba sa tausaya wa talakawa, masu gidan ma wanda kake tsammanin ya ba ka ma bai da shi".

A wajen mutane da dama dai matsin tattalin arzikin da ake fuskanta ya rage wa bukukuwan sallar armashi.