Nigeria ta kara sama a gasar Paralympics a Rio de Janeiro

Tambarin gasar Paralympics
Bayanan hoto,

Najeriya ta kara samun daukaka a gasar Paralympics ta nakasassu

Yanzu haka Najeriya na mataki na tara a jerin kasashen da suka cin lambobin yabo a gasar Paralympics ta nakasassu da ake yi a birnin Rio de Janeiro na Brazil.

A yanzu dai yawan lambobin da kasar ta samu sun kai tara, biyar daga ciki kuwa na zinare ne.

Ndidi Nwosu ce ta ciyo wa Najeriya lambar zinare ta baya-bayan nan bayan da ta sha gaban mai rike da kambun daga nauyi ajin kilogiram 73.

'Yan wasan, wadda da farko ta yi kamar za ta hakura da lambar tagulla ta zage dantse daga karshe ta daga nauyin kilogiram 140, lamarin da ya ba ta damar shan gaban 'yar Faransa Souhad Ghazouani, wacce kafin lokacin ke kan gaba.

A yanzu dai China ce ke kan gaba da lambobi 98—zinare 41, da azurfa 33, da tagulla 24—sai Birtaniya a matsayi na biyu da lambobi 58—zinare 25, da azurfa 14, da tagulla 19.