Nigeria: An yi sallar Idi a garin Konduga na Jihar Borno

Daga dama, Sanata Abubakar Kyari, Gwamna Kashin Shettima, Hakimin Konduga Alhaji Zanna Masu Yale, da sauran jama'a yayin sallar Idin

Asalin hoton, Isa Gusau

Bayanan hoto,

Gwamna Kashim Shettima ya ce za a sake gina makarantu da asibitocin yankin

A wani mataki na nuna cewa komai ya fara komawa daidai a Jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya, a ranar Litinin an gudanar da sallar Idi a garin Konduga, daya daga cikin wuraren da a da suke hannun 'yan Boko Haram.

Gwamnan Jihar ta Borno, Kashim Shettima, da Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kan Al'umma ta Kasa (NOA), Garba Abari na cikin mutanen da suka yi sallar.

Tun shekarar 2014 ne dai kungiyar Boko Haram ke iko da garin na Konduga, inda suka yi barin wuta a kan gine-ginen gwamnati, kama daga asibitoci zuwa makarantu, da gidajen jama'a da kasuwanni.

Sun kuma fatattaki mutane da dama, wadanda suka kwashe kusan shekara biyu suna gudun hijira a Maiduguri.

Gwamna Shettima ya ce ya yi sallar Idi a Konduga ne ba don garin ya fi sauran garuruwan da aka sake kwatowa daga hannun ''yan Boko Haram ba, sai dai "don kusancinsa da Maiduguri, saboda wadanda muka taho da su su samu damar komawa su yanka ragunan layyarsu wadanda galibin suke babban birnin".

Ya kuma ce sun je Konduga ne don su karfafa gwiwar mutanen garin da ba su fi mako biyu da komawa gidajensu ba cewa an samu zaman lafiya.