'Babu hadarin girgizar kasa a jihar Kaduna'

Motsin kasar ya firgita jama'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamnan Kaduna Malam Nasurr El-Rufai

Mahukunta a jihar Kadunan Nigeria sun ce suna gudanar da bincike a kan wata 'yar karamar girgizar kasa da ta auku a kudancin jihar.

Lamarin dai ya auku ne a garin Kwai na karamar hukumar Jaba, kuma ya firgita wasu mazauna yankin, har wasu na fargabar cewa watakila lamarin zai munana ya kai ga haddasa babbar girgizar kasa.

A ranar Lahadi ne dai aka fara fuskantar motsin kasar tsakanin karfe goma na safe zuwa hudu na yamma.

An kuma sake fuskantar wata a ranar Litinin da karfe hudu na asubahi.

To sai dai ba a samu jikkata ko asarar rai ba.

Da dama daga mazauna garin sun tsere zuwa wasu garuruwan, don tsoron kar lamarin ya yi kamari.

Sai dai masana a nasu bangaren na cewa motsin da kasar ta yi ba shi da hadari, kasancewar yankin da abin ya faru bai fada yankunan da masifar kasar kan abka musu ba.

Furofesa Maharazu Yusuf Malami a sashen nazarin bayanin kasa a jami`ar Bayero ta Kano, ya ce bincike ya nuna cewa yanayin karkashin kasa da ake da shi a yammacin Afirka ya sa da wuya a samu girgizar kasa.