'Yara na fama da yunwa a arewa maso gabashin Nigeria'

Yara da dama na fama da tamowa
Bayanan hoto,

Yara na fuskantar barazanar kisa daga yunwa

Wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa yunwa na barazanar kashe yara 50,000 a Najeriya nan da wata 12 masu zuwa, matukar ba su samu kulawar gaggawa ba sadoda tamowa mai tsanani da suke fama da ita .

Babban jami'in da ke kula da samar da abinci mai gina jiki na asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, Arjan de Wagt, ya shaida wa BBC cewa munin lamarin a arewa maso gabashin kasar ya zarta duk yadda ake zato.

Ya ce an gano girman matsalar ne tun bayan da aka fara fatattakar 'yan Boko Haram daga wuraren da suka yi kaka-gida.

Ya ce yara 250,000 na fama da babbar matsalar rashin abinci mai gina jiki a jihar Borno, kuma a duk cikin yara biyar daya na fuskantar barazanar mutuwa.

Mista de Wagt ya kara da cewa wata babbar barazanar da ake fuskanta kuma ita ce yadda ciwon Polio ke sake bulla a yankin.