Tamowa: UNICEF ta ba mu mamaki —Nigeria

Shugaban hukumar NEMA, Muhammad Sani Sidi

Asalin hoton, NEMA

Bayanan hoto,

Hukumar NEMA ta ce rahotannin cewa yara na fuskantar barazanar mutuwa na ba ta mamaki

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa a Najeriya (NEMA) ta ce rahoton da ake fitarwa cewa yara kusan 50,000 ka iya mutuwa saboda kamuwa da tsananin tamowa yana ba ta mamaki.

Hukumar na mayar da martani ne ga babban jami'in Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) mai kula da samar da abinci mai gina jiki, Arjan de Wagt.

Babban jami'in hukumar NEMA mai kula da yankin na arewa maso gabashin Najeriya, Muhammad Kanar, ya shaida wa BBC cewa "...Gwamnatin Najeriya ba ta taba rufe kofarta ba ga wadannan {kungiyoyi da hukumomi} don hada hannu da su wajen gudanar da ayyukanmu. A Borno kawai akwai irin wadannan [kungiyoyi da hukumomi] da muke aiki da su kusan 31".

Ya kuma ce hukumar NEMA na aiki da hukumomi da kungiyoyin agaji na kasashen duniya amma "sai su zo su fid da rahoto kan cewa ga shi yara suna mutuwa, kuma duk inda aka tafi hoto da bidiyo suna nuna cewa wadannan mutanen lafiyarsu kalau".

Ya kara da cewa a Bama aka samu wannan lamari kuma an dauki mataki.

"An je an yi babban asibiti a wurin, an kai masu kaya, kuma abinci ba ya yankewa a Bama, da Banki, da Fulka, da Gwoza", inji shi.

Mista de Wagt ya yi gargadi ne cewa yunwa na barazanar kashe yaran 50,000 a yankin arewa maso gabashin Najeriya nan da wata 12 masu zuwa, matukar ba su samu kulawar gaggawa ba.