Nijar: An kashe sojoji 7 da 'yan BH 15

Sojojin Nijar sun kashen 'yan Boko Haram 15

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sojoji 7 'yan Boko Haram suka kashe

Rundunar Sojin jamhuriyar Nijar ta ce dakarun gwamnatin kasar sun kashe wasu da ake kyautata zaton `yan Boko Haram ne su 15 , sannan kuma sun tabbatar da mutuwar sojoji 7, yayin da wasu 8 suka jikata.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce mayakan Boko Haram din dai sun yi wa sojojin kwanton-bauna ne ranar Litinin a kusa da garin Tumur da ke jahar Difa, inda suka kashe biyar daga cikin dakarun, sannan suka jikkata shida.

Sanarwar da aka fitar ranar Talata a Yamai ta ce, sojojin na Nijar sun maida martani, inda suka kashe 'yan Boko Haram 15, suka kama 2, sannan suka kwace makamai da dama.

Ma'aikatar tsaron ta ce wasu sojojin na Nijar biyu kuma sun mutu, wasu biyun kuma sun jikkata, a yankin Barwa cikin jihar Boso, bayan da motarsu ta taka wata nakiya da aka binne.

Ma'aikatar tsaron ta ce a yanzu haka an kara baza jami'an tsaro a yankin don farautar 'yan Boko Haram.

Ita ma, rundunar tsaron hadin-gwiwa ta fitar da wata sanarwa tana cewa a yanzu 'yan Boko Haram sun rasa katabus sakamakon matsin-lambar da suke fuskanta.

Rundunar hadin-gwiwar ta ce 'yan Boko-haram na mika wuya sakamakon matsin-lamba da rashin abinci.