Syria: An zargi 'yan tawaye da saba yarjejeniyar tsagaita wuta

Rasha ta ce 'yan tawaye suna yi wa yarjejeniyar karan-tsaye

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An shiga rana ta uku a yarjejeniyar tsagaita wuta

Wakilin Majalisar dinkin duniya da ke kula da al`amuran da suka shafi Syria, Staffan de Mistura ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar da ta fara aiki ranar Litinin ta taimaka gaya wajen rage hare-hare a Syria.

Ya ce abu na gaba da ya fi muhimmanci shi ne shigar da kayan agaji birnin Aleppo da ke hannun `yan tawaye.

Sai dai Rasha ta yi zargin cewa `yan tawaye sun saba wa yarjejeniyar har sau ashirin a kasar baki daya, kana ta bukaci Amurka da ta tsawata wa `yan tawayen da take mara musu baya

Kakakin ma`iakatar harkokin cikin gidan Amurka Mark Tuner ya ce suna nan suna sa-ido:

Ya ce a kullum suna aiki a iya hurumin gwamnatin Amurka tare da tuntubar Rasha, suna nazarin rahotannin da ke cewa ana saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma idan suka tabbatar da haka, to suna iya yanke sharawarar warware yarjejeniyar ma baki daya.