An zargi Birtaniya da Faransa da haifar da rikici a Libya

Birtaniya da Faransa ne suka jagoranci hanbarar da shi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An hanbarar da Mu'ammar Gaddafi a 2011

Wani rahoton da majalisar dokokin Birtaniya ta fitar, ya caccaki Birtaniya da Faransa dangane da rawar da suka taka wajen hambare shugaban Libya, Muammar Gaddafi daga kan karagar mulki a shekara ta 2011.

Kamitin harkokin wajen majalisar ya ce son zuciya irin na siyasa ne ya sa shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy amfani da karfin soji wajen tumbuke shugaba Gaddafi da sunan kare farar-hula a Libya.

Kazalika, kwamitin ya zargi tsohon Firayim Minista David Cameron da gazawa wajen yin kyakkyawan tsarin tunkarar rikicin Libya.

A cewar rahoton ba a yi tunanin ya mokamar siyasar kasar za ta kasance ba, sannan sun ce David Cameron shi ne ya ke da alhakin gaza samar da wani tsari da za a daura Libya a kai, abin da suka ce wannan ne ya haifar da rikicin cikin gida, da durkushewar tattalin arziki, da karuwar 'yan ci rani da suka addabi nahiyar turai, da kuma yaduwar kungiyar IS a arewacin Afirka.

Sai dai Kakakin gwamnatin Birtaniya ya ce ai kungiyar kasashen Larabawa da majalisar dinkin duniya su ma sun goyi bayan daukin da Birtaniya da Faransa suka kai Libya

A watan Maris din 2011 ne wani kawancen kasashe da Birtaniya da Faransa suka jagoranta ya kaddamar da hare haren makami mai linzami da kuma jiragen sama a kan dakarun Mu'ammar Gaddafi , bayan gwamnatin ta yi barazanar kai farmaki kan birnin Benghazi wanda yan tawaye suka kwata.

To sai dai Libya ta tsunduma cikin rikice-rikice bayan hanbarar da Gaddafi, inda kuma aka samu gwamnatoci biyu, da daruruwan yan bindiga dadi, yayayin da ita ma kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci take cin karenta ba babbaka.