Shimon Peres na fama da shanyewar jiki

Tsohon shugaban Isra'ila Shimon Peres

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An yi wa Shimon allurar bacci, kuma yana numfashi da taimakon na'ura

An garzaya da tsohon shugaban Israela Shimon Peres asibiti a wajen birnin Tel Aviv bayan gamuwa da shanyewar jiki.

Rahotanni sun ce jikin na sa ya yi tsanani. Ofishinsa ya fitar da wata sanarwa inda yace likitoci sun dukufa domin ceto rayuwarsa.

Ofishin tsohon shugaban ya ce an yi masa allurar bacci, sannan kuma yana numfashi da taimakon na'ura.

Rahotanni sun ce yana fama da mummunar matsalar zubar jini a cikin kwakwalwa, kuma an kwantar da shi a wajen kulawa ta musamman, inda aka dauki hoton sassan jikinsa don gano hakikan abinda ke damunsa.

An jima ana damawa da Shimon a gwamnatocin Israila, ya zama fara minista sau biyu sannan daga baya ya zama shugaban kasa.

A shekarar 2014 ya lashe kyautar Nobel sabo da rawar da ya taka wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Falasdinawa da aka y a birnin Oslo, ya kuma yi taraya a kyautar da Fara minista Yitzhak Rabin wanda aka yi wa kisan gilla, da shugaban Falasdinawa Yasir Arafat.

Ya taba gamuwa da bugun zuciya a farkon wannan shekara, sannan an yi masa tiyata a farkon watannan.

Sai dai duk da shekarunsa, ya ci gaba hada-hada da jama'a, da kuma kokarin kulla alaka ta kusa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.