Ikorodu United ta ci Enyimba 3-2

Firmiya Mako Teburi

Asalin hoton, lmcnpfl

Bayanan hoto,

Ikorodu United ce ta biyun karshe a kan teburi

Ikorodu United ta doke Enyimba da ci 3-2 a kwantan wasan mako na 24 na gasar Premier ta Najeriya da suka buga da yammacin ranar Laraba.

Fatai Abdullahi ne ya fara ci wa Ikorodu kwallo a minti na 29 da fara wasa, amma Enyimba ta farke ta hannun Mfon Udoh a minti na 32, aka je hutu ana kunnen doki.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Balogun Oluwole ya kara ci wa Ikorodu kwallo na biyu; sai dai minti takwas tsakani Musa Najare ya farkewa Enyimba.

Ikorodu ta kara kwallo na uku ta hannun Michael Okoyoh, wanda hakan ya ba ta damar samun maki uku a fafatawar.

Rivers United ce ke mataki na daya da maki 56 a kan teburi bayan da aka yi wasannin mako 35, Rangers ce ta biyu da maki 54, Ifeanyiubah tana da maki 53 a matsayi na uku sai Wikki Tourists da maki 51.