Real Madrid ta ci Sporting 2-1

Ziyarci Karawa Wasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid za ta ziyarci Dortmund a wasa na biyu

Mai rike da kofin zakarun Turai Real Madrid ta fara kare kambunta da kafar dama, bayan da ta doke Sporting Lisborn 2-1 a fafatawar da suka yi a ranar Laraba.

Sporting ce ta fara cin kwallo ta hannun Bruno Cesar minti uku da dawowa daga hutu.

Daf da za tashi daga karawar Cristiano Ronaldo ya farke, sannan Alvaro Morata ya kara ta biyu.

Real Madrid tana rukuni na shida da ya kunshi Legia Warszawa da Borussia Dortmund da kuma Sporting Lisborn.

Borussia Dortmund wadda ta casa Legia Warszawa 6-0 za ta karbi bakuncin Real Madrid a ranar 27 ga watan Satumba.