Muna nan da karfinmu —Boko Haram

Daya daga cikin jagororin Boko Haram
Bayanan hoto,

Wanda ya jagoranci sallar Idin ya ce bidiyon sabo ne ba tsoho ba

Kungiyar Boko Haram ta ce tana nan da karfinta sabanin ikirarin da gwamnatin Najeriya ke yi cewa ta kawo karshen mayakanta.

Kungiyar ta bayyana haka ne a wani hoton bidiyo da ta saka a shafin intanet na Youtube ranar Talata, wanda ya nuna abin da ta kira sallar Idin da suka yi ranar Litinin.

Hoton bidiyon dai ya nuna masallatai uku da aka gudanar da sallar; daya daga cikin masallatan rufaffe ne kuma ya cika makil da mutane.

A hudubar da ya yi, wanda ya jagoranci sallar a rufaffen masallacin ya ce hasali ma 'yan kungiyar ta Boko Haram suna nan cikin koshin lafiya.

Daga karshe kuma ya aike da sako ga babban hafsan rundunar sojin kasa ta Najeriya, Janar Yusuf Buratai, da mukaddashin kakakin rundunar, Kanar Sani Usman Kukasheka.

"Wannan sakon da muka fitar yau, kada fa su ce tsohon sako ne wanda ya wuce a baya: yau ne muka yi shi, ranar Litinin, 12 ga watan September, shekara ta 2016".

Sai dai kuma hoton bidiyon bai nuna shugaban kungiyar, wanda suka ce suna yi masa biyayya, wato Abubakar Shekau, ba.