"An ci karfin 'yan ta'adda a Sahel"

Shugaba Francois Hollande na Faransa

Asalin hoton, PHILIPPE WOJAZER

Bayanan hoto,

Rundunar Barkhane ta sojin Faransa a Sahel ta ce wajibi ne gwamnatoci su tabbatar ana damawa da kowa don hana karuwar ta'addanci

Kwamandan rundunar tsaro ta Barkhane a Sahel, Janar Xavier Woillemont, ya ce 'yan ta'adda ba su da sauran karfin kai hari na a-zo-a-gani wanda zai iya ba su ikon kama wani gari a yankin.

Janar Woillemont ya kara da cewa sabanin yadda mutane ke tunani, rundunonin sojin kasashen yankin na Sahel biyar wadanda suka hada da Burkina Faso, da Cadi, da Mali, da Mauritaniya, da Niger, tare da taimakon rundunar ta Barkhane, na samun galaba a kan kungiyoyin 'yan ta'adda.

Da yake magana a kan yaduwar da kungiyar IS mai da'awar kafa daular Musulunci ta fara yi a yankin, musamman a Burkina Faso inda ta dauki alhakin kai hari a wani ofishin kwastam a farakon wannan watan, Janar Woillemont ya ce idan kasashe suka hada kai za su iya dakile yaduwar kungiyar.

Janar Woillemont ya yi wadannan kalamai yayin da rundunar sojin Nijar ta ce dakarun gwamnatin kasar sun kashe wadansu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne su 15, sojoji bakwai kuma suka rasa rayukansu, yayin da wasu takwas suka jikkata.

Wata sanarwa da ma'aikatar tsaron kasar ta Nijar ta fitar ta ce mayakan Boko Haram din dai sun yi wa sojojin kwanton-bauna ne ranar Litinin a kusa da garin Tumur da ke jahar Difa.

Rundunar Barkhane dai runduna ce ta sojojin Faransa masu kiyaye zaman lafiya a yankin na Sahel.