An zargi wasu kamfanonin Switzerland da sai da gurabataccen mai a Afirka

Famfunan man gas

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An zargi kamfanoni hudu na Switzerland da safarar gurabataccen man diesel zuwa kasashen Afirka takwas

Wani sabon rahoto da wata kungiya mai zaman kanta a Switzerland ta fitar ya zargi wasu kamfanonin kasar da sayar da gurabataccen man makamashi ga kasashen Afirka.

Kungiyar mai suna Public Eye ta yi ikirarin cewa kamfanonin na Switzerland masu sayar da man diesel suna amfani da rashin kwararan dokokin sa-ido don cin kazamar riba daga gurabataccen man mai dauke da gubar da yawanta ya haramta sayar da ita a Turai.

Rahoton ya kuma yi zargin cewa da aka auna samfurin man na diesel a wadansu kasashen Afirka takwas an gano cewa sinadarin farar wutar da ke ciki ya haura adadin da aka amince da shi a Turai har sau 300.

Ko da yake wannan adadin na cikin ka'idojin da dokokin wadannan kasashe suka amince da su, hayakin irin wannan man diesel din na kara yawan kamuwa da cututtukan da suka shafi numfashi irin su asma (asthma) a kasashen da abin ya shafa.

Rahoton ya yi ikirarin cewa kamfanonin Switzerland hudu, Vitol, da Trafigura, da Addax & Oryx, da Lynx Energy sun amfana da wannan harka a matsayinsu na masu hannun jari a kamfanonin da ke raba man diesel din.

Sai dai Trafigura da Vitol sun ce an hada rahoton da wata muguwar manufa, kuma sun yi nesa da 'yan kasuwar da ke bin dokokin kasashen sau-da-kafa.

Uku daga cikin kamfanonin da ke rarraba man sun mayar da martani suna cewa sun cika sharuddan kasuwancin da aka gindaya, kuma babu wani amfani da za su samu daga barin yawan sinadarin sulphur din dake cikin man ya wuce kima.