An ba da rahoton Shema ya kai kansa EFCC

EFCC ta baza komarta kan Shema

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema

Rahotanni daga Nigeria sun ce da safiyar yau tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya kai kansa ofishin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati.

Wadansu majiyoyi a hukumar ta EFCC sun tabbatar wa BBC cewa yanzu haka tsohon gwamnan yana ofishin, inda yake rubuta jawabi ana kuma yi masa tambayoyi.

A jiya ne dai tsohon gwamnan ya musanta sanarwar da EFCC ta fitar ranar Laraba cewa ba ta san inda yake ba, don haka tana neman shi ruwa-a-jallo.

Hukumar dai na neman Shema ne game da zargin yin sama da fadi da wasu makudan kudin Jihar ta Katsina.